in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Likitoci zasu bunkasa fannin lafiya a arewa maso gabashin Najeriya
2016-12-12 10:16:14 cri
Mahukunta a Najeriya sun ce a kalla likitoci 100 asibitin koyar na jami'ar Maiduguri (UMTH) dake jahar Borno a shiyyar arewa maso gabashin kasar ya dauka aiki, domin bunkasa fannin kiwon lafiya da kuma samar da yanayi mai inganci game da sha'ani na kiwon lafiya a jihar.

Ibrahim Kuburu, shugaban kungiyar likitoci na UMTH, ya shedawa manema labarai a Maiduguri cewa, an dauki likitocin aiki ne a bangarori da dama da suka hada da masu aikin tiyata, da masana cukutan ido, da masana kwayoyin cutuka, da masana cutukan kananan yara, da kuma wadan da suka kware wajen daukar hotunan cutukan cikin jikin bil adam, yace an dauke su aiki ne domin cike gibin karancin jami'an kiwon lafiya da asibitin ke fama da shi.

Ya kara da cewa, asibitin yana fama da kalubaloli na yawaitar marasa lafiya wadanda suke gamuwa da raunuka iri dabam dabam, a sanadiyyar hare haren boma boma na kungiyar Boko Haram.

Ya ce kungiyar ta fara wani shiri na ziyartar sassanonin 'yan gudun hijira, musamman yankunan da aka kwato su daga hannun 'yan ta da kayar baya.

Al'amurran kiwon lafiya sun gurgunce a jihohin arewa maso gabashin Najeriya ne, a sakamakon yadda likitoci da ma'aikatan jiyya da kuma masana ilmin hada magunguna ke kauracewa yankunan, domin kaucewa fuskantar hare hare mayakan Boko Haram.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China