Stephane Dujarric ya bayyanawa taron manema labaru cewa, hukumar sa ido kan harkokin cikin gida na MDD ta kammala bincike kan karar da shigar kan ma'aikatan kiyaye zaman lafiya game da cin zarafin fararen hula da dama a kasar Afirka ta Tsakiya daga shekarar 2014 zuwa 2015.
Mr. Dujarric ya bayyana cewa, an mikawa Gabon da Burundi wannan rahoto, yayin da MDD ta bukaci gwamnatocin kasashen biyu da su nazarci rahoton, tare da yin bincike kan wadanda ake tuhuma nan da nan, domin gabatar da sakamakon bincike da za a samu kan wannan batu.
Ban da haka, Mr. Dujarric ya kara da cewa, rundunar sojan kiyaye zaman lafiya ta MDD dake kasar Afirka ta Tsakiya ta dauki karin matakai domin yin rigakafi da sa ido, da ba da agaji ga wadanda aka ci zarafinsu a fannonin tunani, da jiyya, da doka da sauransu tare da sauran hukumomin da abin ya shafa. Ya jaddada cewa, MDD ta yi Allah wadai da babbar murya kan wannan batun cin zarafi, kuma za ta ci gaba da daukar matakai domin tabbatar da ganin an gurfanar da mutanen da ake zargi da aikata wannan danyen aiki a gaban kotu. (Fatima)