Jami'in ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a taron shekara shekara na kungiyar sada zumunta tsakanin Najeriya da Sin karo na 24 a birnin Legas, ya ce a kwanan nan ne suka samu wasu labarai da ake yadawa ta shafukan internet cewa wai akwai wani sabon jakada da ake kira jakadan Taiwan har yana da ofis a Abuja.
"Sam sam ba zai yiwu ba Taiwan ta mallaki ofishin jakadanci Abuja. Sai dai za ta iya kafa ofishin kasuwanci ne kadai a Najeriya", in ji Bola Akinterinwa, kuma tsohon darakta janar a cibiyar nazarin dangantakar kasa da kasa ta Najeriya.
Shi ma tsohon jakadan Najerya a kasar Sin Jonathan Coker, ya ce ya saba ka'ida Taiwan ta nada jakada a Najeriya, ko kuma ta ce za ta kafa ofishin jakadanci.
Sola Onadipe, shi ma tsohon jakadan Najeriya a kasar Sin, ya ce dole ne Najeriya ta yi bincike game da zargin nada jakadan Taiwan a kasar. (Ahamd Fagam)