Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar INEC, ta shirya gudanar da zaben ne bayan wani hukuncin kotun tarayyaar kasar a ranar 19 ga watan Maris inda ta soke zaben majalisun dokokin wanda aka gudanar tun a shekarar 2015.
Sai dai ana fuskantar rikice rikice a lokacin zaben, lamarin da ya tilasta hukumar zaben dakatar da zaben ana tsaka da gudanar da shi.
Wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua dake jahar ya rawaito cewa, an fara zaben ne a kananan hukumomi 8 a jahar, kuma an fara tantance masu kada kuri'a tun da misalin karfe 8:30 na safe. (Ahmad Fagam)