Moshood Jimoh, shi ne kwamandan bataliya ta 31 ta sojojin kasar, ya shedawa manema labarai a Minna babban birnin jahar Niger bayan kammala wani taron tattaunawa game da sha'anin tsaro.
Ya ce tuni hukumomin tsaron suka tanadi matakan tabbatar da tsaro gabanin gudanar da bukuwawan Kirsimeti da lokacin bukukuwan da ma bayan kammala bukukuwan.
A cewar Jimoh tuni aka girke jami'an tsaro a wasu wuraren da ake da fargaba domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali. (Ahmad Fagam)