Shugaban na Afirka ta kudu ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, kwana guda bayan kammala taron koli na dandalin FOCAC wanda ya gudana a birnin Johannesburg.
A yayin taron da ya gabata, shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarwari 10, game da tsarin da za a bi domin bunkasa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka. An kuma fidda sanarwar bayan taro mai kunshe da tsarin inganta hadin kan sassan biyu.
Da yake tsokaci game da hakan, shugaba Zuma ya ce shawarwarin da shugaba Xi ya gabatar sun shaida lura da Sin ke yi ga bukatun Afirka, maimakon zuwa da ra'ayin kashin kai.
Ya ce babu kanshin gaskiya game da rade-radin da kasashen yamma ke yadawa, cewa Sin na gudanar da mulkin mallaka a Afirka, kwatankwacin wanda 'yan mulkin mallaka suka yi a baya, na wawashe albarkatun nahiyar ta Afirka. A cewar sa wasu daga kasashen yamma sun arzuta kan su daga albarkarun nahiyar, ba tare da baiwa Afirka wani tallafi ba. A daya hannun kuwa, Sin na aiwatar da hadin gwiwa da Afirka a dukkanin fannonin ci gaba da suka hada da na siyasa da tattalin arziki da dai sauran su.(Saminu)