Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Wu Haitao ya bayyana a jiya Jumma'a cewa, a sabon yanayin da ake ciki na fuskantar ta'addanci a duniya, ya kamata kasashen duniya su dauki matakai daga dukkan fannoni domin yaki da ta'addanci cikin hadin kai.
A wannan rana, an kira taron MDD, inda aka duba dabarun yaki da ta'addanci na duniya tare kuma da zartas da kuduri. Wu Haitao ya ba da jawabi cewa, ya kamata kasashen duniya su bi ma'auni daya wajen gudanar da aikin yaki da ta'addanci, ya kamata a kawar da dukkan laifuffukan ta'addanci ba tare da kasala ba. Dole ne a bi jagorancin MDD da kwamitin sulhu wajen yaki da ta'addanci bisa ka'idojin kundin tsarin MDD. Sa'an nan, bai kamata a alakanta ta'addanci da wasu kabilu da addinai ba.
Ya kuma kara da cewa, kasar Sin muhimmiyar memba ce a kawancen yaki da ta'addanci na duniya, tana dukufa kan aikin yaki da ta'addanci a ciki da waje. A karshen shekarar 2015, kasar Sin ta kaddamar da dokar yaki da ta'addanci. Za ta ci gaba da rigakafin ta'addanci da kare rayukan jama'ar Sin da kuma dukiyoyinsu. Kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasashen duniya wajen tinkarar kalubalen ta'addanci, domin kara ba da gundummawa wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.(Lami)