Wani fitaccen mai bincike a cibiyar nazarin al'amurran tsaro ta Afrika ta kudu Martin Ewi, ya fada a yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labaraun kasar Sin Xinhua cewar, rashin fuskantar hare haren ta'addanci a kasar Afrika ta kudu ba yana nufin kasar ta tsira daga fuskantar duk wani harin ta'addanci ba.
Martin ya fadi hakan ne bayan da gwamnatin kasar ta nuna halin ko-in-kula da wani gargadin da ofisoshin jakadancin Amurka da Birtaniya dake Afrika ta kudun suka fitar game da barazanar yiwuwar kai hari a kasar.
A cewar gargadin, 'yan ta'adda suna kokarin kaddamar da harin ne a manyan kantunan zamani da kasuwanni, musamman ma a biranen Johannesburg da Cape Town a lokacin azumin watan Ramadan
To sai dai ministan tsaro na Afrika ta kudun David Mahlobo, ya fada a ranar Litinin cewar gwamnatin kasar ta lura da gargadin, amma bai kamata jama'a su tada hankalinsu ba.