Kakakin MDD Stephan Dujarric wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai, ya bayyana cewa, tuni ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Morocco ta sanar da sakatariyar MDD game da matakin da kasar ke shirin dauka, wanda ya hada da rage wakilcinta a shirin na kada kuri'ar raba gardama game da makomar yankin, musamman reshen harkokin siyasa,da kuma kawo karshen irin gudummar da take bayarwa na sama da dala miliyan 3.
A kwanakin baya ne dai Ban Ki-moon ya ziyarci sansanonin 'yan gudun hijira da ke yammacin Sahara, inda ya kwatanta yankin a matsayin wanda aka mamaye shi. Wannan kalami ya haifar da zanga-zanga a Rabat abin da ya sanya gwamnatin Moroccon daukar wannan mataki.
Sai dai kakakin na MDD ya ce, Ban Ki-moon ba zai canja kalaman nasa ba. (Ibrahim)