Mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric, ya shedawa yan jaridu cewa, a karshen makon da ya wuce an cigaba da gwabza kazamin fada, lamarin da ya jefa rayuwar dubban fararen hula a kasar cikin garari.
MDD ta bukaci a tsakaita bude wuta, domin fararen hular su samu damar ficewa daga yankunan da rikicin ya shafa, kana a samu damar kwashe wadanda suka jikkata da kuma kai agaji ga mutane masu rauni.
Kakakin MDD ya ce, majalisar tana cigaba da samun rahotannin dake nuna cewa dubban fararen hular sun fice daga yankunan gabashin Aleppo a karshe mako sakamakon rikicin da ya yi kamari, sai dai ba'a tantance adadin mutanen da suka tsere din ba.
MDD ta ce tana da mutane dubu 40 da suka gujewa rikicin daga gabashin Aleppo dake neman mafaka a wajen da hukuma ta tanada a ranar 9 ga watan Disamba.
Wasu daga cikin mutanen na cigaba da samun mafaka a yankin, yayin da wasu kuma suka cigaba da kwarara zuwa wasu yankunan domin gujewa rikicin.
Ya ce babban abin damuwa shi ne yadda makomar 'yan gudun hijirar za ta kasance a sansanin da aka tanada, sakamakon yanayin sanyi da ake fama dashi a halin yanzu.
Sai dai kakakin MDD ya ce, MDD tana cigaba da hada kai da bangarorin da abin ya shafa domin kai dauki ga fararen hular dake cikin yanayin bukatar agajin abinci, da sutura, da wuraren kwana da kiwon lafiya da kuma abinci mai gina jiki ga kananan yara. (Ahmad)