Wu Haitao, wanda shi ne mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya yi wannan kiran ne a lokacin taron MDD game da batun Syria, inda aka tsayar da kudurin daukar matakan kai agaji ga yankunan dake fama da tashe tashen hankula a kasar ba tare da gindaya wasu sharruda ba.
Ya ce, ya kamata duk wani yunkurin da za'a yi game da rikicin Syria ya kasance sun shafi wadannan batutuwa 4, na farko, maido da batun yarjejeniyar tsakaita bude wuta, tattaunawar hanyoyin warware rikicin kasar ta hanyar siyasa, hada gwiwa don yakar ta'addanci, da kuma neman hanyoyin shigar da agaji kasar. Ya kara da cewa, dole ne Syria ta taka rawa wajen jagorantar wadannan manufofi.
Game da batun rawar da kasashen Rasha da Amurka ke takawa na bin hanyoyin diplomasiyya wajen warware rikicin na Syria, Mista Wu ya ce, dole ne ya kasance duk wani mataki da wani bangare zai dauka ya tabbatar da kare ikon kasa, da 'yancinta, da tabbatar da hada kan kasa da kiyaye ikon Syria, kuma ya kasance yunkuri ne da zai warware matsalar ba sake dagula al'amura ba.(Ahmad Fagam)