in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar 'yan wasan kwallon kafa ta mata ta Najeriya ta ki ficewa daga sansaninsu na horaswa
2016-12-07 19:23:54 cri
Tawagar 'yan wasan kwallon kafa ta mata ta Najeriya wadda ta lashe kofin gasar cin kofin kwallon kafan mata ta Afirka karo na 8, bayan da ta doke 'yan wasan Kamaru a ranar Asabar, ta yi watsi da umarnin da hukumar kwallon kafa ta Najeriyar ta ba su na ficewa daga sansanin su na samun horo da ke Abuja, suna masu cewa, ba za su bar sansanin ba, har sai an biya su hakkokinsu.

'Yan wasan na Super Falcons suna zargin hukumar ta NFF da rashin biyansu kudaden su na alawus, da na alawus din wasa da albashin masu horas da su har na tsawon sama da watanni 8.( The Guardian)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China