in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na fatan sassauta dadadin koma bayan tattalin arziki kan al'umma
2016-12-07 09:46:37 cri
Gwamnatin Najeriya na aiki tukuru domin takaita illolin koma bayan tattalin arziki na yanzu kan al'umma, in ji ministar harkokin mata da ci gaban jama'a madam Aisha Jummai Alhassan a ranar Litinin.

Gwamnatin ta yanzu ta dauki matakai domin rage radadin wahalhalun al'ummar kasar bayan koma bayan tattalin arziki, in ji ministar a yayin wani zaman taron da gwamnatin kasar ta shirya domin fadakar da mutane kan gaskiyar halin da ake ciki na tattalin arziki da kasar take fuskanta da kuma hanyar da za a dauka.

Madam Alhassan ta nuna cewa yana bisa layi guda tare da kokarin da gwamnati take yi domin rage radadin wahalhalun 'yan Najeriya wato gwamnatin ta kafa wani shirin kawo dauki ta fuskar zabu jarin jama'a.

Jami'ar ta bayyana cewa shirin dake kunshe da ginshikai biyar, an tsara shi domin kyautata matsayin tattalin arziki da jama'a na 'yan Najeriya, musammun ma wadanda ba su galihu.

Haka kuma, hukumar kasuwanci da masana'antu ta Lagos (LCCI), ta yi hasashen cewa babbar kasar tattalin arziki ta Afrika ba za ta dauki tsawon lokaci ba kafin sake karbe tsawon matsayinta na alfahari a cikin kungiyar kasashen Commonwealth. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China