in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Minista: Najeriya za ta karbo bashi ne don samar da kayayyakin more rayuwa
2016-12-09 20:39:23 cri
Ministan kasafin kudi da tsare-tsare na Najeriya Udoma Udo Uduma, ya bayyana cewa, Najeriya ta kuduri aniyar karbo rance daga ketare ne da nufin samar da muhimman kayayyakin more rayuwa a sassa daban-daban na kasar.

Ministan wanda ya bayyana hakan yau Jumma'a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, ya ce idan har gwamnatin ta samu amincewar karbo bashin, hakan zai taimakawa kasar ta bunkasa tattalin arziki mai dorewa ta hanyar kammala ayyukan da aka shirya gudanarwa a kasar.

Ministan ya ce tasirin zuba jari yana da muhimmanci matuka, kuma wata kafa ce da za ta dora kasar kan turbar bunkasuwa mai dorewa.

Gwamnatin Najeriyar dai tana neman rancen da ya kai dala biliyan29.9 ne daga abokan hulda na kasa da kasa kamar bankin duniya da asusun IMF.

A halin yanzu dai Najeriya, babbar kasa a nahiyar Afirka, tana fama da karancin kayayyakin more rayuwa, lamarin da ya tilastawa mahukuntan kasar nemo bashi don cike wagegen gibin, sakamakon matsalar tattalin arziki da gazawar kasafin kudin na cike gibin kayayyakin more rayuwar jama'a da ake fuskanta.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China