Muhammad Sani Sidi, darekta janar hukumar kula da matsalolin gaggawa ta kasa (NEMA), ya bayyana cewa kayayyakin agajin an tura su zuwa ga 'yan gudun hijira da suka bar kasar bayan hare-haren a jahohin dake arewa maso gabashin kasar.
Ya bayyana cewa wadannan kayayyakin an samar da su ne musamman ma domin kai dauki ga 'yan gudun hijiran Najeriya, tare nuna cewa Najeriya za ta ci gaba da tabbatar da kula da hadin kai tare da Kamaru domin tabbatar da cewa dukkan 'yan gudun hijira na zaman rayuwa cikin yanayi mai kyau.
Darekta-janar ya tabbatarwa 'yan gudun hijira cewa gwamnatin Najeriya ba ta manta da su ba kuma za ta yi iyakacin kokarin kwashe zuwa jahohinsu na asili. (Maman Ada)