in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya zai yi wa majalisun dokokin kasar jawabi game da matsin tattalin arziki
2016-12-07 10:19:45 cri
Majalisar dattijan Najeriya ta ambato cewa shugaba Muhammadu Buhari na kasar zai gabatar da jawabi ga majalisun dokokin kasar a ranar 14 ga watan da muke ciki game irin matakan da gwamnatinsa ke ci gaba da dauka don fitar da kasar daga halin matsin tattalin arzikin dake damunta.

Shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki, shi ne ya sanar da hakan a zauren majalisar dake Abuja, ya ce shugaban Najeriya zai kuma gabatar wa majalisun dokokin kasafin kudin kasar na shekarar 2017 mai zuwa.

A watan Sabumba ne gwamnatin kasar ta sanar da halin matsin tattalin arziki da take fuskanta a hukumance. Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar ta fitar na baya bayan nan ta nuna cewar karfin tattalin arziki na GDP a kasar ya ragu da kashi 2.24 cikin dari.

Matsin tattalin arzikin da kasar ke fuskanta ya haifar da wasu karin matsalolin da suka hada da tashin farashin kayayyakin masarufi, da raguwar asusun ajiyar kasar na kasashen ketare da kuma faduwar darajar kudin kasar wato Naira.

Bangaren albarkatun mai na kasar wanda shi ne babbar hanyar samun kudin shiga ga kasar ya gamu da cikas, sakamakon faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya, sannan ga matsalar hare haren 'yan ta da kayar baya a shiyyar kudancin kasar dake lalata kayayyakin hako albarkatun kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China