in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ONUSIDA ta yaba sabon shirin yaki da Sida a Najeriya
2016-12-05 10:23:46 cri
Tsarin hadin gwiwa na MDD kan HIV/SIDA (ONUSIDA) ya nuna yabo ga Najeriya bisa matakin da ta dauka na kaddamar da wani sabon shirin da zai taimaka wajen gaggauta daukar nauyi da rigakafin yaduwar HIV a cikin kasar.

Wannan sabon shirin zai taimaka wajen kafa cikin sauri wajen karin kulawa da mutane dubu 500 dake dauke da cutar Sida da kuma taimakawa kasar wajen cimma muradin 90-90-90 da kanta, in ji shugaban sadarwa na ONUSIDA reshen Najeriya, mista Charles-Martin Jjuuko a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.

Muradin 90-90-90 na da burin, nan da shekarar 2020, kashi 90 cikin 100 na mutane da su san matsayinsu na ko suna dauke da kwayoyin cutar Sida, kuma kashi 90 cikin 100 na mutanen da aka gano suna dauke da kwayoiyin cutar su samu kulawa cikin karko, kuma kashi 90 cikin 100 na mutanen da suka samu kulawa a soke musu wani nauyin kwayar cikin karko. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China