A wajen bikin, shugaban babban taron MDD Peter Thomsen ya ce, yarjejeniyar kare hakkin nakasassu da aka zartas shekaru 10 da suka wuce, tamkar ishara ce ga yunkurin tabbatar da daidaitun hakkin nakasassu, sai dai har yanzu ana fuskantar kalubaloli da yawa dangane da wannan aiki. Yanzu a cikin nakasassu biliyan 1 na duniyarmu, kashi 80% na fama da kangin talauci. Saboda haka, jami'in ya bukaci gwamnatoci daban daban da su kara kula da nakasassu, yayin da suke kokarin aiwatar da shirin raya kasa mai dorewa nan da shekarar 2030.
A nasa bangare, mista Ban Ki-moon, babban sakataren MDD, ya bayyana cewa, yarjejeniyar kare hakkin nakasassu ta yi amfani, amma duk da haka har yanzu nakasassu na gamuwa da matsaloli a fannonin samun ilimi, da neman aikin yi, da ganin likita, da dai makamantansu. Saboda haka ya yi kira ga kasashe daban daban da su kara kokari, don kawo karshen bambancin ra'ayi da ake nunawa nakasassu, da kawar da duk wani shinge da suke gamuwa da shi yayin zaman rayuwa, ta yadda ba za a bar su a baya ba a kokarin aiwatar da shirin raya kasa mai dorewa.(Bello Wang)