in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman labarai daga wasu jaridun Najeriya(20161209)
2016-12-09 19:19:26 cri

A jiya ne majalisar dattawan Najeriya ta amince da bukatar da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya mika don gabatar da mata da shirin kasafin kudin kasar na shekarar 2017 a ranar 14 ga wata.(Daily Trust)

Gwamnatin Najeriya ta ayyana cewa, tana nuna shakkun cewa, tawagar 'yan wasan kwallon kafar mata wato Super Falcons ba za ta lashe kofin gasar ta shekarar 2017 ba, don haka ba ta shirya biyan kudaden alawus din 'yan wasan ba.

Ministan watsa labarai na Najeriya Lai mohammed ya baiwa 'yan Najeriya mamaki lokacin da ya ce gwamnati ba ta da kudin da za ta biya alawus din 'yan wasan, wadanda suka doke 'yan wasan kamaru mai masaukin gasar a wasan karshe da suka buga.(The Guardian)

An kara tsaurara matakan tsaro a jihar Rivers, musamman birnin Fatakwal dake Tarayyar Najeriya, gabanin zaben cike gurbi na majalisar dokokin jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Nnamdi Moni ya bayyana cewa, an jibge jami'an tsaro ne don tabbatar da cewa, an gudanar da zaben na gobe Asabar ba tare da wata matsala ba.(The Punch)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China