in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman labarai daga wasu jaridun Najeriya
2016-12-06 19:18:44 cri
Gwammnatin Najeriya ta ce daga watan gobe ta haramta shigo da motoci ta kan iyakokin kasar. Wannan sabuwar doka ta hada da sabbi da kuma motocin da aka yi amfani da su.

Wata sanarwar da hukumar hana fasa-kauri ta Najeriyar ta fitar a jiya Litinin, ta yi nuni da cewa, harancin shigo da motocin ya biyo bayan umarnin da shugaban kasar ya bayar ne cewa, daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2017 za a rika shigo da motocin ne kadai ta tashoshin ruwa kasar.(The Punch)

Gwamnan babban bankin Najeriya Goodwin Emefiele ya bayyana cewa, duk da matsalar tattalin arzikin da kasar ta tsinci kanta a ciki wanda ba a taba ganin irinsa a tarihi ba. Lamarin ya haidar da damammakin inganta makomar kasar a nan gaba.

Gwamnan babban bankin kasar ya kuma yarda cewa, ana fama da matsalar karancin kudi,faduwar farashin mai, wanda shi ne abin da kasar ta dogara da shi wajen samun kudaden musayar ketare da kudaden shigar gwamnati,ya ragu matuka, kuma hakan na iya kasance na dogon lokaci.Don haka ya yi kira ga 'yan kasar da su canja halayensu.(The Guardian)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China