in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya gana da shugaban Gabon
2016-12-09 10:39:49 cri

Da yammacin jiya Alhamis ne, firaministan majalisar gudanarwa ta kasar Sin Li Keqiang ya gana da shugaban kasar Gabon Ali-Ben Bongo Ondimba a birnin Beijing, wanda ke ziyarar aiki a nan kasar Sin.

Firaminista Li ya bayyana cewa, Sin za ta yi hadin gwiwa da Gabon a fannonin raya tattalin arziki, da kyautata rayuwar jama'a, da kara karfin samun dauwamammen ci gaba, da samun daidaito kan manufofin bunkasuwa domin kara raya albarkatun makamashi bisa tsarin kasuwanni, da kafa manyan kayayyakin amfanin jama'a, da bunkasa aikin noma da sha'anin gandun daji da dai sauransu. Sabon jirgin saman da kasar Sin ta yi nazarin kerawa da kanta na da tsaro da inganci da kuma araha, wanda zai biya bukatun kasashen Afirka na raya zirga zirgar jiragen sama a shiyya shiyya. A sabili da haka, bangarorin biyu za su iya yin shawarwari kan hadin gwiwa tsakaninsu a wannan fanni.

A nasa bangare, shugaba Bongo ya bayyana cewa, an sami ci gaba sosai wajen inganta hakikanin hadin gwiwa tsakanin Gabon da Sin, wadanda suka yi mu'amala sosai kan harkokin duniya da na shiyya shiyya. A sabili da haka, dangantaka tsakaninsu ta zama abin koyi ga sauran kasashen duniya. Yanzu Gabon na cikin muhimmin lokaci na canza hanyar raya tattalin arzikinta, da fatan yin hadin gwiwa da Sin a fannonin samar da muhimman kayayyakin amfanin jama'a, da raya aikin gona da sha'anin gandun daji, da bunkasa sha'anin sufurin jiragen saman da dai sauransu. Gabon tana maraba da kamfanonin Sin wajen zuba jari a kasar, domin yin amfani da sabon zarafin bunkasuwa tare da juna.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China