in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya gana da shugaban Saliyo
2016-12-02 21:42:16 cri

A yammacin jiya Jumma'a, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da shugaban Saliyo Ernest Bai Koroma a birnin Beijing, wanda yake ziyarar aiki a nan kasar Sin.

A yayin ganawar tasu, firaminista Li ya bayyana cewa, a ranar daya ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari da mista Koroma, tare da samun sakamako mai kyau. Kasashen biyu za su kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a duk fannoni. Sin na fatan zurfafa amincewar juna a fannin siyasa, da karfafa hakikanin hadin gwiwa tsakaninta da Saliyo, da kara yin mu'amala da hadin gwiwa kan harkokin shiyya shiyya da na duniya baki daya, da zummar kara kawo alheri ga jama'ar kasashen biyu.

Ban da haka kuma, firaminista Li ya bayyana cewa, Sin na fatan zurfafa hadin gwiwa a fannonin kafa manyan kayayyakin amfanin jama'a, da masana'antu, da hakar ma'adinai, da aikin gona da dai sauransu. Sin tana fatan kara hadin gwiwa da Saliyo a fannin kiwon lafiya, kamar ba da horo ga likitocin Saliyo, da tura tawagar likitoci zuwa Saliyo da dai sauransu.

A nasa bangare, shugaba Koroma ya nuna godiyarsa ga gwamnatin kasar Sin wajen ba da jagoranci kan taimakawa kasar wajen yaki da cutar Ebola, da kara karfinta na yin rigakafi da shawo kan cututtuka. Ya ce, akwai dankon zumunci tsakanin kasashen biyu. Saliyo na fatan koyon fasahohin bunkasuwar kasar Sin, da kara yin hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin kafa manyan kayayyakin more rayuwa, da sha'anin ma'adinai, da aikin gona da sauransu, da yin hadin gwiwa a sabon fannoni na sadarwa, da kiwon lafiya, da yawon shakatawa da sauransu, domin sa kaimi ga bunkasa dangantaka tsakanin Saliyo da Sin zuwa wani sabon mataki.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China