in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya halarci bikin bude taron inganta harkokin kiwon lafiya na duniya karo na 9
2016-11-22 10:52:01 cri

A jiya Litinin, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya halarci bikin bude taron inganta harkokin kiwon lafiya na duniya karo na 9, kana ya gabatar da jawabi.

A jawabin da ya gabatar, Li Keqiang ya nuna fata ga kasa da kasa su kara yin shawarwari kan tsara manufofi da kafa dandalin hadin gwiwa na kiwon lafiya, da kara wakilcin kasashe masu tasowa da basu ikon tofa albarkacin bakinsu, da sa kaimi ga yin hadin gwiwa da kafa tsarin kiwon lafiya da yin rigakafi da yaki da cututtuka na duniya, da inganta karfin tinkarar lamuran kiwon lafiya da suka faru ba zato ba tsammani a duniya, da sa kaimi ga yin hadin gwiwa a fannin kirkire-kirkire, da kara karfin samar da hidimar kiwon lafiya, da musayar fasahohi da juna, da sa kaimi ga bunkasuwar ilmin kiwon lafiya na gargajiya da na zamani bai daya.

Li Keqiang, ya yi nuni cewa, Sin kasa ce da take bin hanyar sa kaimi ga kiwon lafiya da ya dace da yanayinta. A shekarar 2009, Sin ta tabbatar da maida tsarin kiwon lafiya a matsayin aikin more rayuwa na zamantakewar al'umma, inda ta kafa tsarin kiwon lafiya dake shafar mutane fiye da biliyan 1 da miliyan 300, wanda ya samar da tabbaci ga duk wanda ke fama da ciwo a kasar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China