Jiya Talata aka kaddamar da cikakken taro karo na farko game da rigakafi da magance cututtuka masu tsanani cikin hadin gwiwa dake tsakanin hukumomin gwamnatin kasar a karkashin jagorancin majalisar gudanarwar kasar Sin, da taro karo na uku na kwamitin aikin rigakafi da magance ciwon kanjamau na majalisar gudanarwar kasar ta Sin a nan birnin Beijing, inda zaunannen mamban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma firayin ministan kasar Li Keqiang ya ba da muhimmin urmuninsa kan aikin.
Li Keqiang ya bayyana cewa, kara karfafa aikin rigakafi da kuma magance manyan cututtuka, musamman ma ciwon kanjamau yana da muhimmanci matuka, ga aikin kiyaye tsaron lafiyar al'ummar kasar, a saboda haka kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwar kasar Sin suna mai da hankali sosai kan aikin. Yayin da aka gudanar da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar na 12 a kasar ta Sin, hukumomin gwamnati na matakai daban daban na kasar sun yi kokari matuka, kuma sun samu babban sakamako, ya kamata a yaba da aikinsu a fannin. Yanzu ana kokarin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar na 13, ya zama wajibi a kara mai da hankali kan aikin, tare da jagorancin ajandar MDD game da kawo karshen yaduwar ciwon kanjamau nan da shekarar 2030, kana a dauki matakai a jere, misali tantance jini, da hana yaduwar ciwon tsakanin mahaifiya da jariri, tsara manufofin samar da tallafi ga masu ciwon, da samar da isashen kudin jinya, da hanzartar da nazari kan magunguna, da kara karfafa hadin gwiwa dake tsakanin kasa da kasa a fannin, da samar da tallafi ga kungiyoyin sa kai domin su gudanar da aiki yadda ya kamata, da dai sauransu, da haka za a cimma burin hana yaduwar ciwon a kasar ta Sin, tare kuma da kara kyautata lafiyar jikin al'ummar kasar.(Jamila)