in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya gana da Antonio Guterres, mai jiran gadon babban sakataren MDD
2016-11-29 10:54:27 cri

A jiya Litinin da yamma, Mr. Li Keqiang, firaministan kasar Sin ya gana da Antonio Guterres, mai jiran gadon babban sakataren MDD a nan Beijing.

Da farko dai, Mr. Li Keqiang ya taya wa Antonio Guterres murnar zama sabban babban sakataren MDD, yana kuma fatan MDD ta ci gaba da kare da kuma bin ka'idojin "Kundin Mulkin MDD" domin tabbatar da ganin kasashe mambobin MDD sun yi zama daidai wajen daidaita harkokin kasa da kasa, da kuma nuna goyon baya ga kokarin kara wakilci da ikon gabatar da ra'ayoyi na kasashe masu tasowa a lokacin da ake daidaita harkokin kasa da kasa. Sannan Mr. Li Keqiang yana fatan MDD za ta iya tabbatar da ganin an aiwatar da ajandar neman ci gaba ba tare da wata tangarda ba kamar yadda ya kamata. A waje daya, za ta iya daukar matakan siyasa a lokacin da take kokarin daidaita rikice-rikicen da suke kasancewa a wasu kasashe cikin lumana.

Bugu da kari, Mr. Li Keqiang ya nuna cewa, kasar Sin, wato kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, kuma mambar dindindin ta kwamitin sulhu na MDD, za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da sassa daban daban wajen nuna goyon baya ga kokarin tabbatar da mutuncin MDD da kara karfinta wajen tinkarar kalubaloli iri daban daban, da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da dawaumammen ci gaba a duniya baki daya.

A nasa bangare, Mr. Antonio Guterres ya bayyana cewa, kasar Sin ta samu ci gaban da ke jawo hankulan duk duniya, kuma rawar da take takawa a duniya tana ta samun karfafuwa, har ma tana taka muhimmiyar rawa a lokacin da ake daidaita harkokin MDD. Ya kara da cewa, MDD ta yaba wa bangaren Sin wajen aiwatar da ajandar neman ci gaba tare da wata tangarda ba, kuma tana fatan kara yin hadin gwiwa da bangaren Sin domin tinkarar kalubalolin da suke kasancewa cikin hadin gwiwa, da kuma bunkasa tattalin arzikin duk duniya bai daya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China