A wannan rana da safe, jiragen saman yaki guda biyu dake dauke gawawwakin 'yan wasan kungiyar ta Chapecoense AF da suka mutu a sakamakon hadarin jirgin sama sun iso filin jiragen sama na Chapecó, daga baya an kai su zuwa filin wasa dake birnin. An ce, mutane fiye da dubu biyu ne suka taru a filin wasan, ciki har da iyalan 'yan wasan da suka mutu, da mazaunan birnin Chapecó, da kuma masu sha'awar kungiyar daga wurare daban daban daga sassa na duniya.
A wajen bikin, dukkan jama'a sun yi shiru na tsawon minti guda don nuna ta'aziyya ga 'yan wasan da suka mutu. Shugaban kasar Brazil Michel Temer, da shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino da kuma magajin garin birnin Chapecó sun halarci bikin.
A daren ranar 28 ga watan Nuwanba ne, jirgin saman dake dauke da 'yan wasan kungiyar Chapecoense AF da 'yan jarida ya yi hadari, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 71. (Zainab)