Gidan radiyon kasar Argentina ya sanar cewa, dan wasan gaban na Barcelona da sauran yan wasan kungiyar na cigaba da karbar magani bayan amai da suka sha fama da shi.
Jagoran tagawar yan wasan Jorge Miadosqui, ya furta cewa "da gaske ne jirgin yayi tangal tangal, har tasa yan wasan sun kadu matuka lamarin da yasa suka kamu da rashin lafiya, amma wannan ba sabon abu bane idan har kana tafiya a cikin jirgin sama zuwa San Juan".
Sai dai babu koda guda daga cikin yan wasan da ya yi hasartar wasan da zasu buga na share fagen shiga gasar kwallon kafan ta duniya da zasu kara.
A halin yanzu, Kungiyar wasan Edgardo Bauza tana matsayi na 6 cikin kungiyoyin yan wasa 10 na shiyyar kudancin Amurka, inda ta samu maki 16 cikin wasanni 11 data buga.
Kungiyoyin yan wasa 4 dake kan gaba ne kadai zasu samu damar tsallakawa don shiga gasar kwallon kafa ta duniya da za'a gudanar a kasar Rasha a shekarar 2018.(Ahmad Fagam)