161027-Messi-da-Ronaldo-sun-sake-shiga-takarar-lambar-Ballon-dOr-zainab.m4a
|
Messi dan kasar Argentina, wanda a bara ya karbi wannan lamba har karo 5, da Rolando dan kasar Portugal wanda ke rike da wannan lamba karo 3, su kadai ne wadanda a baya suke rike da wannan lamba, a kuma yanzu suke sake nema cikin jerin 'yan kwallon 30.
A kungiyar Barca, Messi tare da abokan taka ledar sa Luis Suarez da Neymar, wadanda sune suka fi cin kwallaye a bana, suna cikin wannan jadawali, baya da Andres Iniesta da shi ma ya shiga wannan takara.
A bangaren kungiyar Real Madrid kuwa, Ronaldo tare da sauran 'yan wasa 6 ne ke cikin wannan jadawali. 'Yan wasan dai sun kunshi Wales winger, da Gareth Bale, da Toni Kroos, da Luka Modric, da Sergio Ramos da kuma Pepe.
A tsagin masu taka leda a gasar firimiyar Ingila kuwa, akwai 'yan wasan Leicester City biyu, wato Riyad Mahrez da kuma Jamie Vardy.
An dai fara bayar da Ballon d'Or ne a shekara 1956, domin sakawa 'yan wasa da suka yi fice wajen taka leda cikin shekara guda, bayan da 'yan jaridar nahiyar Turai suka tantance kwarewar 'yan wasan.
A shekarar 2010 ne kuma hukumar FIFA karkashin jagoranta na lokacin Sepp Blatter, ta biya kudi har euro miliyan 15, a matsayin damar bada wannan kofi karkashin hukumar ta FIFA, a kuma wannan lokaci ne aka hade waccan lambar ta yabo ta kasar Faransa, da lambar gwarzon shekara na FIFA, wanda aka fara bayarwa tun daga 1991 ya zuwa 2009, inda kuma bisa sabon tsarin masu horas da 'yan wasa na kasa da kasa, da jagororin kafofin watsa labarai daga sassa daban daban ke zabar wanda zai karbi lambar.
Sai dai kuma a 'yan makwannin baya, kafar watsa labaran wasanni ta kasar Faransa mai alaka da shirya wannan biki na mika lambar yabon Ballon d'Or, ta ce ba za a sabunta yarjejeniyar gudanar da bikin karkashin hukumar FIFA ba.(Saminu Alhassan)