Shugaban tawagar yan wasan kasar ta Uganda Milutin Sredojevic, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kungiyar wasan ta shirya tinkarar manyan kungiyoyin wasannin, kuma zasu yi kyakkyawan amfani da irin kwarewar da suka samu a lokacin bada horon domin shiga gasar kwallon kafa mafi girma ta nahiyar Afrika wanda za'a gudanar a kasar Gabon.
Uganda ta samu nasarar shiga gasar ta 2017 AFCON ne, bayan da ta doke Comoros da ci 1-0 a wasannin da suka buga a a watan jiya, bayan da kasar ta shafe shekaru 39 ba tare da shiga gasar ba. Kungiyar wasan ta Cranes, ta buga wasanta na karshe ne a shekarar 1978, bayan data kwashi kashinta a hannun Ghana mai masaukin baki da ci 2-0 a wasan karshe.
Cranes wacce ke a zaune a Port Gentil a lokacin gasar ta AFCON a Gabon, tana rukuni daya da kasashen Masar, Ghana da Mali.
Uganda ce kasa daya tilo cikin kasashen gabashi da tsakiyar Afrika da kungiyar wasan kwallon kafarta ta samu nasarar shiga gasar wasannin kwallon kafa ta 2017 AFCON, wanda za'a gudanar a badi.
Hukumar kula da kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Uganda tuni ta gabatar da kasafin kudi na dala miliyan guda ga gwamnatin kasar, wanda zata yi amfani da kudaden wajen horas da yan wasanta a Dubai, da kuma gudanar da al'amurran gasar wasannin ta AFCON.(Ahmad Fagam)