in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar ta doke Ghana 2-0 a wasan neman gurbin cin kofin duniya
2016-11-16 15:59:07 cri
Kungiyar wasan kwallon kafar kasar Masar ta doke takwararta ta Ghana da ci 2 da nema, a ci gaba da buga wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018 da za a yi Rasha. An dai buga wasan ne a filin wasa dake birnin Alexandria.

'Yan wasan Masar din Mohamed Salah, da kuma Abdullah al-Saeed ne suka ciwa kungiyar su kwallayen. Sakamakon da kuma ya baiwa Masar din damar shigewa gaba da maki 6 a teburin rukunin E. sauran kasashen da ke rukunin sun hada da Uganda da kuma Congo.

Yanzu haka dai kasashen nahiyar Afirka 20 ne ke fafatawa a zagaye na 3 kuma na karshe, a wasannin neman gurbin gasar ta cin kofin duniya, wadda hukumar FIFA ke shiryarwa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China