in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wu Lei ya shiga jerin sunayen 'yan takarar gwarzon dan wasan kwallon nahiyar Asiya a wannan karo
2016-11-16 15:59:47 cri

Daya daga shahararrun 'yan wasan kwallon kafar kasar Sin Wu Lei, ya shiga jerin sunayen da aka gabatar, na wanda zai zamo gwarzon dan wasan kwallon kafar nahiyar Asiya a wannan karo. Sauran 'yan takarar biyu sun hada da Omar Abdulrahman dan wasan hadaddiyar daular Larabawa, da kuma Hammadi Ahmed na kasar Iraki.

Jin wannan labara ya sa Wu Lei farin ciki matuka, inda ya bayyana cewa ya ji dadin wasannin farkon rabin shekarar bana, sabanin wasannin da ya buga a rabin karshen shekarar. Ya ce dalilin da ya sa ya shiga jerin sunayen wadannan 'yan takara shi ne, irin rawar da ya taka a wasannin cikin gida na kasar Sin da ya buga.

Wu Lei ya zamo daya daga 'yan wasa mafiya cin kwallaye a kasar Sin cikin shekaru hudu a jere. Sai dai duk da hakan dan wasan na ganin Omar Abdulrahman dan wasan hadaddiyar daular Larabawa ya fi sauran 'yan takarar damar samun wannan lambar yabo. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China