Jiya Talata, tashar intanet ta jam'iyyar CDU ta kasar Jamus ta labarta cewa, shugabar gwamnatin Jamus madam Angela Merkel ta sake zama shugabar jam'iyyar sakamakon samun yawan kuri'un da yawansu ya kai kashi 89.5 cikin 100 a yayin taron wakilan jam'iyyar wanda aka gudanar a wannan rana a birnin Essen da ke yammacin kasar, lamarin da ya sa madam Merkel ta zama 'yar takarar neman zama shugabar gwamnatin kasar a shekarar 2017 a matsayin jam'iyyar ta CDU.
A cikin jawabinta bayan da ta sake zama shugabar jam'iyyar a yayin taron, madam Merkel ta ce, ta amince kuma ta yi farin ciki da ganin sakamakon, sannan ta godewa wakilan jam'iyyar wadanda suka ba ta amincewa.
A ranar 20 ga watan Nuwamban bana, madam Merkel ta sanar da shiga babban zaben Jamus na watan Satumban shekarar 2017, a kokarin sake zama shugabar gwamnatin kasar. Madam Merkel ta zama shugabar gwamnatin Jamus tun daga watan Nuwamban shekarar 2005. Idan ta sake lashe babban zaben na shekarar 2017, to, za ta fara wa'adin aikinta karo na 4 a matsayin shugabar gwamnatin kasar. (Tasallah Yuan)