in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 10 sun hallaka, sannan wasu 16 sun samu raunuka a harin Munich
2016-07-23 13:08:22 cri

Da safiyar yau Asabar jami'an 'yan sandan kasar Jamus sun fada cewa a kalla mutane 9 ne suka mutu, sannan wasu 16 suka samu raunuka a lokacin wani hari a birnin Munich a shiyyar kudancin Jamus da yammacin jiya Jumma'a, kana daga bisani maharin ya harbe kansa da kansa.

Jami'in 'yan sandan birnin Munich Hubertus Andrae, ya fada a taron manema labaru cewar an gano maharin dan shekaru 18 ne, kuma yana da takardun shedar zama dan kasashen Jamus da Iran, sannan yana zaune a Munich sama da shekaru biyu ke nan.

Andrae ya ce uku daga cikin wadanda suka samu raunuka suna cikin matsanancin hali, kuma daga cikin wadanda suka jikkata har da kananan yara.

Sai dai an gano maharin shi kadai ya kaddamar da harin. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China