in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jamus za ta dauki matakai domin inganta tsaron kasar, in ji shugabar gwamnatin kasar
2016-07-29 11:05:53 cri

Shugabar gwamnatin Jamus madam Angela Merkel, ta yi tir da hare-haren ta'addanci da aka kaddamar a kwanan baya a kasarta, tare da sanar da shirin yaki da 'yan ta'adda da inganta tsaron kasar.

Madam Merkel ta bayyana hakan ne a ranar 28 ga watan nan, yayin taron manema labaru da ya gudana a birnin Berlin, fadar mulkin kasar. Ta ce matakan da za a dauka za su shafi fannoni 9, wato sassauta matakan mai da 'yan gudun hijira zuwa kasashensu na asali, da yin amfani da dabarun gaggawa na gano barazanar cusa tsauraran ra'ayoyi a zukatan 'yan gudun hijira, da gudanar da hadin gwiwar 'yan sanda da sojoji wajen tabbatar da tsaro. Sauran sun hada da amfani da bayanan yaki da ta'addanci kan yanar gizo karkashin shugaban kungiyar Tarayyar Turai cikin hanzari da dai sauransu.

Ko da yake matsalar 'yan gudun hijira tana adabar Jamus sosai a fannin tsaro, amma madam Merkel ta nuna kyakkyawan fata game da makomar kasarta wajen tinkarar matsalar.

Bisa labarin da jaridar duniya ta Jamus ta bayar kan shafin ta na internet a ranar 28 ga wata, an ce, wani sabon binciken ra'ayin jama'a ya nuna cewa, yawancin 'yan Jamus suna ganin cewa, manufar madam Merkel dangane da matsalar 'yan gudun hijira ta ci tura. Fiye da rabin wadanda aka zanta da su na ganin cewa, madam Merkel ba ta kula da damuwar al'ummar kasar. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China