in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Merkel ta sanar da sake neman tazarcewa a matsayin shugabar Jamus
2016-11-21 11:05:03 cri
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sanar da shiga takara a zaben shugaban kasar da za a gudanar a watan Satumba na shekarar 2017 a hukunce a birnin Berlin a daren ranar 20 ga wannan wata.

Merkel ta bayyana cewa, a cikin shekaru 11 da suka gabata, ita da gwamnatin kasar dake karkashin jagorancinta sun cimma wasu nasaori. Yanzu ta sani, idan ta sake zama shugabar kasar, yaya za ta ci gaba da gudanar da harkokin kasar.

Merkel ta ce, wannan ne zaben da ake fuskanta cikin mawuyacin hali mafi tsamani bayan da kasar Jamus ta samu 'yancin kai, domin tilas ne a daidaita bukatun jam'iyyun daban daban na kasar. Game da batun 'yan gudun hijira, ana bukatar kasar Jamus da ta fitar da manufofi masu dacewa.

Madam Merkel mai shekaru 62 da haihuwa ta zama shugabar gwamnatin Jamus tun daga watan Nuwanba na shekarar 2005. Idan ta cimma nasarar zaben da za a gudanar a shekarar 2017, wannan ne karo na hudu da take rike da wannan kujera. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China