Ban da haka kuma, kwamitin sulhun ya nuna damuwarsa game da yadda ake samun karuwar ayyukan ta'addanci, da aikata laifuka a wurare daban daban na kasar Mali, musamman ma a tsakiya da kudancin kasar, gami da yadda rikici ke kara tsananta tsakanin al'ummomin dake tsakiyar kasar.
A cewar kwamitin sulhun, akwai babban nauyi na tabbatar da kwanciyar hankali da tsaro a wuyan gwamnatin kasar.
Haka zalika, kwamitin sulhun na ganin cewa, har yanzu tawagar wanzar da zaman lafiya dake aiki a kasar Mali ko (MINUSMA), ba ta da cikakken karfi na aiwatar da ayyukanta yadda ya kamata, don haka a cikin sanarwar, kwamitin ya bukaci babban magatakardan MDD da ya dauki matakin da ya wajaba cikin sauri.(Bello Wang)