Sanarwar ta bayyana cewa, harin da aka kaiwa tawagar MINUSMA a ranar 3 ga watan nan, ta haddasa kisan jami'an kiyaye zaman lafiyar 'yan asalin kasar Chadi su biyu.
Mambobin kwamitin sulhun MDDr sun jajantawa iyalan mutanen da suka mutu, da gwamnatin kasar Chadi, da tawagar MINUSMA, tare da jinjinawa jami'an kiyaye zaman lafiyar da suke gudanar da ayyuka a kasar. (Zainab)