Don haka, a yayin wani taron manema labaru da aka saba shiryawa a yau 12 ga wata, kakamin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, bangaren Sin yana maraba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar Sham da kasashen Rasha da Amurka suka sake daddalewa. Kakakin ta nuna cewa, tsagaita bude wuta da dakatar da amfani da karfin tuwo, muhimman sharudda ne ga kokarin warware batun Sham a siyasance, kuma matakai ne da suka wajaba da kuma ya kamata a dauka, domin kyautata halin jin kai da ake ciki a kasar Sham, da kuma yaki da ta'addanci kamar yadda ake fata.
Jami'ar kasar ta Sin ta ce "muna fatan bangarori daban daban na kasar Sham za su cimma nasarar aiwatar da abubuwan da yarjejeniyar ta tanada, domin kyautata halin da ake ciki a kasar kamar yadda ya kamata". Bugu da kari, bangaren Sin yana fatan gamayyar kasa da kasa za su goyi bayan shirin aiwatar da yarjejeniyar, a kokarin kafa wani kyakkyawan yanayi ga shirin sake shiga shawarwarin shimfida zaman lafiya a kasar Sham ba tare da bata lokaci ba. (Sanusi Chen)