in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman labarai daga wasu jaridun Najeriya(20161205)
2016-12-05 20:24:16 cri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana tabbacin cewa, gwamnatinsa ba za ta bar 'yan kasar yunwa ta halaka su ba.

Kakakin fadar shugaban kasar Garba Shehu shi ne ya bayyana hakan a jiya Lahadi, yayin da ya ke mayar da martani ga gargadin da wasu hukumomi suka yi cewa, yunwa za ta halaka mutane kimanin miliyan guda a yankin arewa maso gabashin kasar a shekara mai zuwa. (Daily Trust)

Ministan lafiya na Najeriya Isaac Adewole ya ce, 'yan kasar da dama suna mutuwa sakamakon cin abincin da bai kamata. Ya kuma bayyana cewa, cututtuka kamar su shanyewar bangaren jiki, hawan jinni, bugun zuciya, ciwon suga da sauransu za su yi haddasa hasarar da ta kai sama da dala biliyan 8 a cikin shekaru 10 masu zuwa a kasar.(Vanguard)

Manoma da masu samar da kayayyaki da sauran masu ruwa da tsaki a Najeriya suna kassara kokarin gwamnatin kasar na fadada sassan tattalin arzikin kasar tare da rage dogaro kan shigo da kayayyaki, yanzu haka, wadannan bangarori sun fi son yin musayar kudaden ketare wajen shigo da muhimman kayayyaki, maimakon sayar da kayayyakin ga 'yan kasa a farashin kasuwa.

Rahotanni na nuna cewa, manoma da sauran masu samar da albarkatu na sayar da kayayyaki fiye da farashin da gwamnati ta kayyade, kuma hakan na iya haddasa hauhawar farashin kaya, musamman yadda ake fama da karancinsu da bukatarsu a kasashe makwabta.(Guardian)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China