Amurka da Rasha sun bukaci fara aiki da matakin tsagaita wuta a Syria daga bakin ranar Litinin mai zuwa, in ji shugaban diflomasiyyar Amurka.
Samun shiga ta hanyar karfafa da karko wajen isar da agajin jin kai na kasancewa wata bukatar gaggawa a yankunan dake cikin yaki, musammman birnin Aleppo, in ji mista Kerry.
Wasu jerin shawarwari da dama sun gudana tsakanin shugabannin Amurka da Rasha ta fuskar diflomasiyya a tsawon makwanni biyu na baya bayan nan domin kai ga cimma wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Syria. A matsayin wani sakamakon na tsawon shawarwarinsu na baya baya, manyan jami'an biyu sun cimma ra'ayi kan yiyuwar wani aikin soja cikin hadin gwiwa domin yaki da ta'addanci a kasar Syria, idan har an samu tsagaita wuta a tsawon kwanaki bakwai a jere wanda kuma gwamnatin Bashar al-Assad da kuma 'yan adawa ya kamata su girmama. (Maman Ada)