in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Sama da dala biliyan guda ake bukata don bada tallafi a arewa maso gabashin Najeriya
2016-12-03 13:17:40 cri

Mai magana da yawun MDD yace ofishin jin kai na MDD na bukatar kimanin dalar Amurka biliyan guda a shekarar 2017 mai kamawa, domin amfani da kudaden wajen samar da tallafi ga mutane sama da miliyan 7 dake cikin halin matsi a jihohi 3 na arewa maso gabashin Najeriya da matsalar hare haren Boko Haram ta fi shafa wato jihohin Borno da Yobe da Adamawa.

Stephane Dujarric, ya shedawa 'yan jaridu cewa, koda yake dakarun tsaron Najeriya sun yi nasarar kwato dukkannin yankunan dake karkashin ikon Boko Haram, sai dai mazauna yankunan na cikin wani mummunan hali da suke bukatar a kai musu daukin gaggawa.

Peter Lundberg, shi ne ko'odinetan ofishin jin kai na MDD a Najeriya ya ce, wannan ita ce matsala mafi girma a nahiyar Afrika, amma a cewarsa idan kasashen duniya da hukumomi masu zaman kansu suka tallafa, za'a iya shawo kan halin da mazauna yankunan na arewa maso gabashin Najeriyar ke ciki.

Mutane miliyan 4.6 ne ke fama da yunwa a arewa maso gabashin kasar, kuma daga cikin adadin mutane miliyan 2 na bukatar kai musu daukin gaggawa. A wasu yankunan kuma, kashi 50 cikin 100 na kananan yara na matukar fama da karancin abinci mai gina jiki.

A cewar wata kididdiga game da yanayin tsaro da aka gudanar ta nuna cewa, daga watan Augusta, mutanen dake cikin yanayin bukatar agajin gaggawa a jahohin Borno da Yobe da Adamawa ya ninka har sau biyu, wato daga mutane miliyan 1 zuwa mutane miliyan 1 da dubu 800.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China