in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masani:Hunkuncin da aka yanke kan batun tekun kudancin kasar Sin ba shi da tushe
2016-07-18 13:06:27 cri
Jaridar Jama'a mallakar gwamnatin kasar Aljeriya, ta fidda wani bayanin da Ismail Debesh, farfesa mai nazarin ilimin siyasa na jami'ar kasar Algiers ya rubuta a ranar Asabar, wanda ya bayyana cewa hukuncin da aka yanke kan batun tekun kudancin kasar Sin ba shi da tushe ko kadan, kuma sakamako ne da aka samu bisa radin kan kasashen yammacin duniya.

Masanin ya ce, cikin mambobi masu shari'a 5 na kotun da aka kafa, 4 sun fito ne daga kasashen yammacin duniya, yayin da dayan ya dade yana zaune a nahiyar Turai, duk da kasancewarsa dan asalin nahiyar Afirka ne. Kana shaidun da aka gabatar na cike da kura-kurai masu yawa, don haka ba za su tabbatar da komai ba.

Cikin bayaninsa, Ismail Debesh ya ce, tsibiran dake tekun kudancin kasar Sin sun dade suna karkashin mallakar kasar Sin, domin tarihi ya nuna cewa jama'ar kasar sun fara gano tsibiran, da amfani da su, tun fiye da shekaru dubu 2 da suka wuce. Yayin da a bangaren Phillipines, ba ta da wani bayanin da ya shafi tsibiran, cikin yarjeniyoyin shata iyakar kasar ta, wadanda ta kulla tare da sauran kasashe masu ruwa da tsaki a shekaru fiye da 10 da suka wuce.

A cewar masanin, don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan shiyya, ya kamata a girmama ikon mulkin kasashen da batun ya shafa, da cikakkun yankunansu. Kaza lika akwai hakikanin shaidun da suka tabbatar da cewa tsoma bakin da kasashen da ke waje da wata shiyyar suke yi, zai iya haifar da babbar matsala, wadda za ta yi daidai da tsoma bakin da kasashen yammacin duniya suka yi wa kasashen Iraki, Libya, da Sham.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China