in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumomin MDD sun yi kira da a kara yawan tallafin da ake samarwa ga 'yan gudun hijirar Sahrawi
2016-11-03 10:30:03 cri
Shirin samar da abinci na duniya, da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR, tare da asusun yara na MDD UNICEF, sun yi kira ga masu ruwa da tsaki da su kara yawan tallafin da suke samarwa ga 'yan gudun hijirar dake zaune a yankunan yammacin saharar Afirka.

Sassan uku sun bayyana cewa, tsawon shekaru 40 da suka gabata, 'yan gudun hijirar al'ummar Sahrawi mazauna saharar dake kudu maso yammacin kasar Aljeriya, na dogaro ne kan tallafin da ake samar musu daga sassan masu bada agajin jin kai.

Rahotanni sun bayyana cewa, wadannan al'ummu na zaune ne a wasu sansanoni 5 wadanda ke kusa da garin Tindouf, cikin wani yanayi mai matukar bukatar tallafawa.

Kungiyoyin sun ce yara kanana, da mata masu juna biyu da masu shayarwa, da tsaffi da marasa lafiya, na cikin wadanda suka fi bukatar tallafin gaggawa.

Da yake karin haske game da hakan, wakilin hukumar UNHCR a Aljeriya Hamdi Bukhari, ya ce a yayin wani zama da ya gudana a birnin New York, wasu kasashe sun sha alwashin samar da karin tallafi ga wadannan 'yan gudun hijira. Mr. Bukhari ya ce yanzu haka ana cikin matukar bukatar tallafi, duba da cewa karancin kudade, ya fara yiwa ayyukan samar da abinci da na kiwon lafiya tarnaki, baya ga karancin wuraren kwana da ruwan sha mai tsafta da ake fama da su.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China