161207-Kungiyar-wasan-kwallon-kafan-mata-ta-Nijeriya-ta-zama-zakara-a-gasar-cin-kofin-Afirka-mata-ta-2016-zainab.m4a
|
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya halarci bikin rufe gasar kallon da aka kawo karshenta.
Kungiyoyi 8 sun halarci gasar a wannan karo, wadanda suka raba a cikin rukunoni biyu. A rukunin A, ya kunshi Kamaru, Masar, Zimbabwe, Afirka ta Kudu. Kana rukunin B, ya hada Nijeriya, Mali, Kenya da Ghana. Kamaru da Nijeriya sun zama matsayin farko a rukuninsu da shiga wasan dake kusa da na karshe, kuma sun cimma nasarar wasan tare da kuma fafatawa a wasan karshe.
Hukumar wasan kwallon kafa ta Afirka na shirya gasar cin kofin Afirka mata a shekaru biyu biyu tun daga shekarar 1998. (Zainab)