in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Najeriya sun damke mayakan Boko Haram 37 a kudu maso yammacin kasar
2016-11-18 11:02:36 cri
Wani sojin Najeriya yace a kalla mayakan Boko Haram 37 sojojin kasar suka cafke a jahohin Legas da Ogun dake shiyyar kudu maso yammacin kasar cikin watanni 15 da suka gabata.

Kwamandan rundunar soji ta 81 mai barin gado manjo janar Isidore Edet, ya shedawa yan jaridu a Legas birnin kasuwancin kasar cewa, an kama yan ta'addan ne a wurare dabam dabam a jahohin biyu.

Jami'in yace, rundunar sojin zata cigaba da farautar mayakan na Boko Haram tare da mika su ga hukumomin da abin ya shafa.

Hukumomi a Najeriya na cigaba da daukar kwararan matakan da nufin murkushe kungiyar Boko Haram. Dakarun Najeriyar na matukar samun galaba a yakin da suke na kakkabe mayakan Boko Haram a duk fadin kasar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China