A watan Oktoba ne dai shugaban ya nemi amincewar 'yan majalisar domin karbo rance daga wasu hukukomin kudi na kasa da kasa da nufin samar da muhimman kayayyakin more rayuwa a kasar. Amma a ranar 1 ga watan Nuwamba sai majalisar ta yi fatali da bukatar karbo rancen saboda abin da aka kira rashin cikakkun bayanai.(Daily Trust)
Fadar shugaban Najeriya tana shirin shimfida bututun mai daga Jamhuriyar Nijar zuwa matatar mai da ke garin Kaduna, sakamakon kalubalen da kasar ta ke fuskanta na tura danyen man daga kudancin kasar zuwa matatar tace mai dake Kaduna.
Babban manajan kamfanin samar da mai na Najeriya Maikanti Baru wanda ya bayyana hakan a karshen mako, ya ce shirye-shiryen gwamnatin tarayyar Najeriya na shimfida bututun mai na tsawon kimanin kilomita 1,000 daga Jamhuriyar Nijar zuwa matatar mai da ke garin Kaduna sun yi nisa.(Vanguard)