in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman labarai daga wasu jaridun Najeriya
2016-12-02 19:27:50 cri
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayyana cewa, kafin zuwan gwamnatinsa, cin hanci da rashawa sun zama tamkar al'ada a kasar. Sai dai ya ce, yanzu haka 'yan kasar suna goyon bayan shirinsa na yaki da wannan annoba, inda yanzu haka ake gudanar da bincike tare da hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki.(Daliy Trust)

A wani labarin kuma, shugaba Najeriyar ya yi kira ga kungiyoyin kabilu masu dauke da makamai da ke neman ballewa da su kwana da sanin cewa,ba mai raba Najeriya.(The Punch)

A jiya ne masana harkar tsaron zirga-zirgar jiragen sama suka yi gargadin cewa,akwai yiwuwar kai hare-haren ta'addanci a filayen saukar jiragen saman kasar, fiye da yadda hukumomin suke zato.

Kwararrun sun bayyana haka ne, bayan labarin gano gawar wani mutum da ya yi satar shiga jirgin saman Arik Air(The Guardian)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China