Bikin nune nune na WAPIC, gaggarumin biki ne mafi girma da ake gudanar a yammacin Afirka a fannin wutar lantarki. Taken bikin a wannan karo shi ne "Ba da jagoranci kan sabon ICT, domin samar da yanar gizo ta wutar lantarki dake hada juna". Shahararrun masana a wannan fanni daga kasashen yammacin duniya sun yi shawarwari kan zamanin sauyawar sabbin fasahohi, da yadda za a yi amfani da kayayyakin ICT da hanyoyin daidaita matsaloli domin kafa yanar gizo ta wutar lantarki mai inganci dake hada juna, da zummar shigar da rayuwar jama'a cikin sabon zamanin makamashi.(Fatima)