in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci a samar da tallafi ga Somaliya
2016-12-03 13:20:48 cri

Babban jami'in bada agaji na MDD dake kasar Somaliya ya bukaci hukumomin dake samar da kayayyakin jin kai dasu samar da tallafi don magance matsalar kuncin rayuwa da al'ummar Somaliya ke fama da ita sakamakon matsalar mummunan fari.

Jami'in jin kan na MDD a Somaliya Peter de Clercq, ya bayyana a birnin Nairobi game da halin matsi da iyalai masu karamain karfi ke ciki a kasar Somaliya.

Jami'in ya ce, ofishin samar da jin kai na MDD ya bukaci kimanin dala miliyan 885 ne a shekarar 2016, amma kashi 47 cikin 100 na kudaden ne aka samu, a yayin da ya rage makonni 4 shekarar ta 2016 ta kare, kuma a cewarsa matsalar farin na cigaba da ta'azzara tare da jefa dubban 'yan kasar ta Somali cikin halin kuncin rayuwa na matsalar karancin abinci da ruwan sha.

Mista Peter, ya bukaci a kai daukin gaggawa domin tinkarar matsalar fari da ta addabi kasar ta Somaliya, ya kara da cewa matsalar farin ta fi kamari ne a yankunan Puntland da Somaliland, amma daga bisani matsalar ta cigaba da yaduwa zuwa wasu sassa na kudanci da tsakiyar kasar ta Somaliya.

A cewar MDD mutanen kasar Somaliya miliyan 5, wato sama da kashi 40 cikin 100 na 'yan kasar ne ke fama da matsalar karancin abinci.

Bugu da kari, sama da yara dubu 320 na fama da karancin abinci mai gina jiki, sannan sama da yaran dubu 50 ne suka fi shiga cikin matsanancin halin karancin abinci mai gina jiki.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China