in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU da dakarun sojin Somali zasu bullo da dabarun murkushe Al-Shabaab
2016-11-25 10:13:27 cri
Dakarun aikin wanzar da zaman lafiya na tarayyar Afrika dake Somaliya (AMISOM), da jami'an sojoji, da kuma manyan kwamandojin rundunar sojin gwamnatin Somali (SNA), sun cimma matsaya don yin aiki tare wajen bullo da sabbin dabarun murkushe mayakan kungiyar Al-Shabaab.

Wani babban jami'in sojin kasar ta Somali, wanda ya kammala taron tattaunawa na kwanaki 3 a Mogadishu, ya ce za su yi aiki tukuru domin tabbatar da kwato yankunan dake karkashin ikon mayakan Al-Shabaab.

Kungiyar tarayyar Afrika ta fada cikin wata sanarwa da ta fitar a Mogadishu cewa, manyan kwamandojin sojin zasu hadu domin kammala shirye shiryen da suka dace don fara aikin.

Sanarwar ta kara da cewa, daga cikin muhimman batutuwan da suka tattauna a loakcin taron na kwanaki 3, sun hada da yadda za'a karfafa rundunar sojin ta SNA, a daidai lokacin da AMISOM ke shirye shiryen kawo karshen wa'adin aikinta a kasar Somali a shekarar 2018.

Daga cikin dabarun janye dakarun aikin wanzar da zaman lafiya na tarayyar Afrikar, kwamitin tsaron na AMISOM ya bukaci a fara janyen dakarun dubu 22, ciki har da na Kenya a farkon watan Oktoba na shekarar 2018, kuma a kammala janyensu zuwa karshen shekarar 2020.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China